Makarantar Islamiyya a Bukuru ta rufta

Hakkin mallakar hoto google maps

Da yammacin lahadin nan ne dai ginin makaranatar ta Islamiyya ya rufta kan dalibai, yayin da suke daukar darasi.

Kawo yanzu hukumomi sun tabbatar gano akalla gawwakin kananan yara hudu da wasu karin biyar da suka jikkata.

Akwai dalibai da baraguzan ginin suka danne sai dai ana dai ci gaba da kokarin zakulo su.

Wani wanda ke kusa da makarantar a lokacin da ginin mai hawa daya ya rufta ya ce lamarin ya faru ne yayin da ake ruwan sama.

Jami'in hukumar agjin gaggawa ta Nijeriya shiyyar arewa ta tsakiyar Nijeriya Alhaji Abdussalam Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin.