"Za mu kai masu laifukan zabe kotu"

Hakkin mallakar hoto inec
Image caption Amina Zakari ta ce sun kammala shirye-shiryen yin zabukan Kogi da Bayelsa.

Shugabar riko ta hukumar zaben Najeriya, Hajiya Amina Zakari ta ce hukumar na gab da gurfanar da mutanen da aka samu da laifukan zabe, a lokacin zabukan da aka yi a watan Maris da Aprilun 2015 a gaban kotu.

Ta ce hukumar ta samu mutane da dama wadanda ake zargin sun tafka laifukan zaben da suka hada da satar akwatunan zabe da raba kudade da ma sauransu.

Amina Zakari ta kara da cewa babu gudu babu ja baya dangane da yunkurin da hukumar ke yi na hukunta masu laifukan.

Shugabar rikon kwaryar ta ce hukumar ta kammala shirye-shiryen sake yi wa mutane da za su kada kuri'a a zabukan gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa rajista, a shirye-shiryen da take yi na gudanar da zabuka a jihohin.

Hukumar ta ce ta kuma bude wani dandali da zai ba da damar sauya katunan zabe ga masu kada kuri'a a jihohin, wadanda yanzu suke wasu jihohin amma suke son komawa jihohonsu domin zabe.