Za a yi bincike a kan hatsarin Makka

Image caption Sarki Salman na Saudiyya

Sarki Salmana na Saudiyya ya ce za su yi bincike dan gano musabbabin faruwar hadarin rikitowar kungiyar da ta yi sanadiyyar mutuwar mahajjata sama da 100.

Ya fadi hakan ne yayin wata ziyarar gani-da-ido da ya kai zuwa babban masallacin da hadarin ya faru, ranar Asabar.

Sarki Salmana ya ce ya je masallacin ne domin ya gane wa idanunsa abin da ya faru da kuma yadda ya faru.

Ya kara da cewa, "Biranen Makka da na Madina sun kasance wuraren da suka fi ko'ina a fadin duniya mahimmanci a gare mu saboda haka za mu bincika kuma za mu sanar da mutane sakamakon binciken".

Kawo yanzu dai an ba wa mahajjata damar ci gaba da ibada a wurin da al'amarin ya faru.

Sai dai kuma har yanzu wani bangaren masallacin yana ci gaba da kasancewa a killace.

Hukumomi a kasar sun ce za a ci gaba da aikin hajji.