Shin ko cin ayaba fiye 6 zai iya hallaka ka?

Image caption Ayaba

A wasu lokutan ana cewa cin ayaba da dama lokaci guda abu ne mai hadari, ana kuma hasashen cewa cin ayaba fiye da 6 a lokaci guda kan iya hallaka mutum.Shin ko akwai gaskiya a cikin wannan magana?

Ayaba na daga cikin 'ya yan itatuwa masu farin jini sosai a duniya, saboda su na da sinadaran gina jiki irinsu Vitamins da kuma Minerals. Shin ko me ya sa wasu suke ganin cewa ayaba na da hadari?

Wani fitaccen mutum da ya rika yada wannan magana shi ne Karl Pilkington, da ke da kusanci da Ricky Gervais mai wasan barkwanci.

" Ina da kwakkwarar hujja, a kan cin ayaba fiye da 6, zai iya hallaka ka, inji Pilkington" a tattaunawar da su ka yi da Gervais da kuma abokin wasan barkwancinsa Stephen Merchant.

"A bayyane take cewar , sinadarin gina jiki na Potassium na karuwa a jikin mutum idan ya ci ayaba guda 6 kuma abu ne da kan iya janyo illa ga lafiyarsa...Na taba ganin kwanon da aka saka ayaba 6 a ciki. Shin ko ka san dalilin da ya sa ayaba 6 ne aka saka a cikin kwanon? Saboda ayaba 7 kan iya janyo illa ga lafiyar dan Adam.

Shin ko wanne irin lahani sinadarin Potassuim ke yi ? A bayyane take cewa sinadarin yana da matukar alfanu ga rayuwar dan Adam a cewar Catherine Collins, kwararriya a kan abinci mai gina jiki a asibitin St George da ke birnin Landan.

A bangare guda kuma idan sinadarin Potassuim ya yi yawa sosai ko aka samu akasin haka a jikin dan Adam to zai iya janyo ciwon zuciya da ciwon ciki da amai da gudawa. Sinadarin Potassuim chloride na cikin sinadarai masu lahani da ake amfani da su a allurar kashe mutane a Amurka saboda idan aka ba mutum fiye da kima yana janyo bugun zuciya.

Sai dai ga mutum mai koshin lafiya"abu ne mai wuya ya ci ayaba da kan iya kawo illa ga lafiyarsa", a cewar Collins." Za ka bukaci ayaba 400 a kowace rana da zasu iya tara sinadarin Potassuim a cikin jiki da kan iya janyo bugun zuciya.......Ayaba ba ta da illa ga lafiyar mutum, tana da amfani sosai ga lafiyar dan Adam.

A cewar hukumar lafiya ta Burtaniya ya kamata manya su rika shan sinadarin Potassuim a kowace rana. Madaidaiciyyar ayaba mai nauyin gram 125 na kunshe da miligram 450 na sinadarin Potassuim, abin da hakan ke nufi shi ne mutum mai koshin lafiya zai iya cin ayaba fiye da 7.

Sai dai akwai wasu mutane da ya kamata su kauracewa nau'ukan abinci masu yawan sinadarin Potassuim, a cewar Collins-kamar masu ciwon koda.

Ire -iren wadannan mutane kodarsu ba ta aiki yadda ya kamata, kuma sinadarin na taruwa a cikin jininsu saboda basa iya fitar da shi idan suka zo yin fitsari".

Ta taba samun wani marasa lafiya da ake tace jininsa wanda ya kamu da bugun zuciya bayan ya ci tumatir mai yawa sosai wanda shi ma 'ya yan itace ne da ke da sinadarin potassuim mai yawa sosai. Kodarsa biyu sun daina aiki shi ya sa ya kasa rage yawan sinadarin Potassuim da ke cikin jikinsa.

Wanu abu da ke janyo damuwa game da ayaba shi ne tana dauke da wani sinadari mai birbishin makamashin nukiliya wanda yasa har ma hukumar dake nazari kan makamashin nukilya ta Amurka ta yi gargadin cewa yawan birbishin makamashin zai iya tunzura nau'rorin da ake amfani da su dom gano makamashin nukiliya da aka yi fasa kaurinsu.

Sai dai Collins ta ce " Yawan sinadarin ba abin damuwa ba ne". Ayaba ba ta da yawan birbishin makamashin nukliya kamar gyadar Brazil watau Brazil nuts kuma ba ta da wani lahani ga lafiya idan aka ci su yadda ya kamata.