'Boko Haram sun fara mika wuya'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rundunar sojin ta ce sojoji suna samun galaba a kan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce 'yan kungiyar Boko Haram da dama sun fara mika wuya sannan wasu ma suna da niyyar yin hakan a nan gaba kadan.

Kakakin rundunar sojin kasan Najeriya, Kanar Sani Kuka-sheka Usman, ya shaida wa BBC cewa hakan na cikin nasarorin da rundunar take samu a kan 'yan kungiyar ta Boko Haram sakamakon daukar sabbin matakan da ta yi dna dakile ta'addanci a kasar.

A cewar sa, matakan sun hada da kai hare-hare ba kakkautawa -- ta sama da kasa -- da kuma toshe kafofin da za su iya samun mafaka ko kayan masarufi.

Kanar Usman bai fadi adadin 'yan kungiyar da suka mika wuyan ba, amma ya ce suna da dama kuma an sami akasarin su ne daga bangaren Bama da Gwoza na jihar Borno.

Ya kara da cewa bayanan da aka samu daga wajen mutanen da suka mika wuya sun nuna cewa akwai wasu da yawa da su ma suke neman hanyar da za su ajiye makamansu.

Gwamnatin kasar dai ta fito da wani shiri na rage wa 'yan kungiyar ta Boko Haram tsananin kaifin kishin addini, ta hanyar sauya musu tunaninsu a kan rayuwa.