Shugaba Buhari zai kai ziyara Faransa yau

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari da Francois Hollande

A yau ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku kasar Faransa.

Wata Sanarwa daga fadar shugaban kasar ta ce shugaban zai gana da takwaransa na Faransa, Francois Hollande kuma za su tattauna ne a kan yadda kasashen biyu za su hada gwiwa domin shawo kan matsalolin tsaro da inganta kasuwanci.

Shugaba Buhari zai kai ziyarar ce bisa gayyatar sa da shugaba Hollande ya yi.

Cikin jami'an da zasu raka shugaban na Najeriya akwai mai bai wa shugaban shawara kan sha'anin tsaro, da kuma wasu jami'an ma'aikatar kudi dana ma'aikatar harkokin waje.

Shugaba Buhari zai kuma gana da wasu jakadun kasashen Afrika a kasar ta Faransa lokacin ziyarar.