Dalibai takwas sun mutu a ruftawar ginin Bukuru

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ginin ya rufta ne a lokacin da ake sheka ruwa.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce izuwa yanzu dalibai takwas ne suka mutu bayan ruftawar da ginin wata makarantar Islamiyya ya yi a Bukuru da ke jihar Filato ranar Lahadi.

Jami'in hukumar, Mohammed Abdulsalam, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa mutane 24 -- 21 mata da maza uku -- sun samu raunuka, kuma an kai su asibiti.

Ya ce ba su san dalilin ruftawar ginin ba, sai dai ya kara da cewa watakila azuzuwan da aka kara ginawa a saman makarantar ne suka sa ginin ya rufta.

Wani wanda ke kusa da makarantar a lokacin da ginin mai hawa daya ya rufta ya ce lamarin ya faru ne yayin da ake ruwan sama.