Majalisar koli da JNI sun sasanta a kan ranar sallah.

Sultan Muhammad sa'ad Abubakar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sultan Muhammad sa'ad Abubakar

Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta janye ranar Laraba da kungiyar Jama'atul Nasrul Islam JNI, ta saka a matsayin ranar babbar sallah watau Eidel Kabir.

Sakataren Majalisar koli kan harkokin musulunci, Ishaq Oloyede, ya ce JNI ta yi kuskure a sanarwar da ta fitar kan ranar sallah.

Ya kuma ce Majalisar za ta fitar da sanarwa ranar Litini game da sabon watan Dhul hajj.

Oloyede ya ce kwamitin duban wata na Majalisar ya amince da matakin da hukomomin Saudiyya suka dauka a kan cewa ranar Talata ce daya ga watan Dhul hajj.

Ya ce ranar Eid-el-kabir za ta kasance 24 ga watan Satumba yayin da 23 ita ce ranar Arafat.

A ranar Lahadi ne Jama'atul nasrul Islam ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana ranar Litinin a matsayin ranar daya ga watan Dhul hajj kuma ta bayyana Laraba a matsayin ranar babbar sallah.