Jamus za ta sa ido kan kalaman batanci a Facebook

Image caption Ana samun yawaitar kalaman batanci a shafin Facebook na Jamus

Jami'an da ke kula da shafin Facebook a kasar Jamus sun ce suna kokarin kafa wani kwamitin cika aiki wanda zai yi yaki da kalaman batancin da ake yi a kan masu 'yan gudun hijira wadanda ake likawa a shafin.

Jami'an sun ce ana samun karuwar kalaman da ke nuna wariyar launin fata da kyamar bakake a shafin na Facebook a Jamus, wanda ke zuwa a daidai lokacin da ake kara samun kwararar 'yan gudun hijira.

Shafin Facebook ya ce zai kara tsaurara matakai don sa ido da kuma kawar da kalaman batanci nan da nan sakamakon matsin lambar da yake samu daga gwamnatin Jamus.

A baya-bayan nan dai dubban 'yan gudun hijira sun shiga Jamus daga Syria, a kokarinsu na gujewa yaki da ya ki ci ya ki cinyewa a kasarsu.