Niger: Hama Amadou ya tsaya takara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Hama Amadou da matarsa da hannu a safarar jarirai.

A Jamhuriyar Nijar, jam'iyyar Moden Lumana ta zabi shugaban majalisar dokokin kasar da ke gudun hijira, Hama Amadou, a matsayin dan takararta na shugabancin kasa a zaben da za a yi a shekarar 2016.

A wata sanarwa da shugabannin jam'iyyar suka fitar sun ce, "Mun yanke shawarar tsayar da Hama Amadou a matsayin dan takararmu na zaben shekarar 2016 ne saboda shi ne mafita ga 'yan Nijar."

An tsayar da Hama Amadou takarar ne a wani taro da jam'iyyar ta gudanar a birnin Zinder.

Shi ne mutum na farko da aka sanar da yin takararsa a zaben da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.

A watan Agustan shekarar 2014 ne Hama Amadou ya fice daga kasar zuwa Faransa bayan an zarge shi da hannu a safarar jarirai.

Tsohon shugaban majalisar dokokin ya sha musanta zargin, yana mai cewa shugaban kasar Mahamadou Issoufou ke yi masa bi-ta-da-kulli.