BH:Kawunan 'yan arewa sun rabu a Lagos

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Video
Image caption Wasu dai sun ce 'yan Boko Haram suna shiga Legas

Wata baraka ta kunno kai a tsakanin sarakunan arewacin Najeriya mazauna birnin Legas, a yayin wani taro da rundunar 'yan sanda ta kira a kan yaki da Boko Haram a jihar.

Rikicin dai ya faru ne a dai-dai lokacin da kwamishinan 'yan sandan jihar ya kira shugabannin arewa domin hada hannu da jami'an tsaro domin hana duk wani yunkurin shigowar 'yan Boko haram jihar.

Wani dai daga cikin mahalarta taron ne ya yi farat ya tashi, sannan ya fada wa kwamishinan 'yan sandan cewa 'yan arewa ba su da jagora a jihar.

Yanzu haka dai mutane biyu ne suke ikrarin sarautar Hausawa a jihar a inda kowanne daga cikin biyun yake cewa shi ne jagora.

Sai dai kuma wasu sun yi amanna cewa 'yan Boko Haram suna shiga birnin na Legas kuma wasu daga cikin al'ummar ta arewa suna ba su mafaka.