Matsalar lambobin sirrin a shafin Ashley Madison

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A na satar bayanai daga shafin Ashley Madison

Sama da lambobin sirri miliyan 11 ne aka sata daga shafin masoya na Ashley Madison na intanet.

Wani gungun masu yin kutse domin satar lambar sirrin mutane ne ya fadi hakan.

Da farko an kasa satar bayanai daga shafin saboda ana tunanin ba za a iya yin kutse ba a cikin lambobin sirrin saboda yadda aka tsara su .

To amma kuma daga baya al'amarin ya sauya saboda sake yi wa shafin fasali da masu kula da shi suka yi, al'amarin da ya ba wa barayin lambobin sirrin damar yin kutse har ma su saci bayanai.

Gungun masu kutsen lambobin sirrin dai sun ce ba za su ba wa kowa lambobin sirrin da suka sata ba.

Sai dai kuma masu satar bayanan sun bayyana irin salon da suka yi amfani da shi wajen satar lambobin sirrin abin da zai ba wa masu kutsen bayanai damar kwaikwayon su wajen satar.

Hakan dai yana nufin duk mutanen da suka sake yin amfani lambobin sirri na shafin na Ashley Madson za su iya ganin an yi wa wasu mutane kutse.

Hakkin mallakar hoto Hoang Dinh Nam AFP GETTY
Image caption An saci kimanin lambobin sirri miliyan 11

Wata kungiya mai suna ' The Impact Team' ita ce ta yi wa shafin na Ashley Madison a inda ta saci bayanai masu nauyin gigabytes da suka hada da sunayen mutane da ake amfani da kuma lambobin sirrin na mutane sama da miliyan 30.