"'Yan gudun hijira za su iya shiga tasku"

Image caption Wasu 'yan gudun hijira daga Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa dubban 'yan gudun hijira za su iya shiga tsaka-mai-wuya dangane da dokokin kula da su, a yayin da kasashen Turai ke bullo da ka'idoji daban-daban a iyakokinsu domin hana su shiga cikin su.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyan ta yi kiran a kafa manyan cibiyoyin karbar 'yan gudun hijira a kasahen Turai da 'yan hijirar ke fara isa.

Kasashen Jamus da Austria da jamhoriyar Czech sun kara tsaurara matakan rufe iyakokinsu a karshen mako.

Jamus ta ce yawan 'yan gudun hijira da suke shiga kasar ya sa ta fara shiga cikin takura.

Kimanin 'yan gudun hijira dubu 16 ne suka shiga birnin Munich na kasar a karshen mako.