Sojoji sun lalata sansanonin Boko Haram

Image caption Bama bamai da Boko Haram ke amfani da su

Sojojin Najeriya sun yi ikirarin lalata sansanonin kungiyar Boko Haram guda hudu a yankunan Banki da Kumshe da Bama na jihar Borno.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Kanar Sani Kukasheka Usman ya fitar ta ce sojojin sun lalata sansanonin a Bolungu ta daya da ta biyu, da Bula Doye da kuma Cheehi Dare.

Sojojin sun kuma kwato wata gada mai muhimmanci da ta hada garuruwan Miyanti da Banki a jihar Borno.

Sanarwar ta ce sojojin sun ceto mata da yara da dama da 'yan kungiyar suka yi garkuwa da su.

Kazalika sanarwar ta ce za a ci gaba da luguden wuta -- ta sama da ta kasa -- a kan mayakan kungiyar har sai an kawar da su.