Rikici ya barke a Congo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Joseph Kabila na son yin tazarce

Mummunan tashin hankali ya barke yayin da 'yan jam'iyyar adawa na Congo suke gangami a Kinshasa babban birnin kasar.

Kimanin mutane 3,000 ne suka taru domin yi zanga-zangar adawa da shirin shugaba Joseph Kabila na yin tazarce zuwa shekarar 2016.

Wakilin BBC ya ce daga baya sai taron ya zama rikici kuma mutane suka fara guduwa saboda tsoron cewa magoya bayan gwamnati masu dauke da makamai za su far musu.

An yi wa wani mutum duka a wajen saboda sun yi amanna yana daga cikin matasa sojojin sa kai masu goyon bayan gwamnati.