El Rufai ya kaddamar da shirin samar da ilimi kyauta

Nasir el Rufai
Image caption Gwamna Nasir el Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el Rufai ya kaddamar da shirin samar da ilimi kyauta a makarantun furamare da kuma sakandire a sassa daban- daban na jihar.

Malam Nasir ya ce gwamnatinsa za ta kashe naira biliyan 9 a kowace shekara wajen samar wa yaran makarantun furamare sama da miliyan daya da abinci kyauta.

Ya kuma kara da cewa shirin zai taimaka wa iyaye wajen rage yawan kudaden da suke kashewa a kan ilimin yaransu.

Gwamanan ya ce za'a dauki teloli dubu biyar aiki wadanda zasu dinka wa yara tufafin makaranta da za'a rarrabawa dalibai da ke sassan jihar daban- daban.

A baya dai tsohuwar gwamnatin jihar Kaduna ta jamiyyar PDP ta kaddamar da shiri makamanci wannan sai dai bai yi tasiri ba.