'Saudiyya ta saki 'yan Nigeria da aka kama'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mahjjatan Najeriya za su shiga jirgin sama

Hukumomi a Najeriya sun yi karin haske game da tsare wasu mahajjatan kasar a gidan fursuna da jami'an tsaro suka yi a kasar Saudiyya.

Jagoran tawagar jami'an kiwon lafiya na hukumar alhazan Najeriya ya ce askarawa sun kama mahajjatan Najeriyar su shida da -- ciki har da wasu likitoci na hukumar alhazan kasar -- ne a lokacin da suke kokarin zuwa wasu yankuna na Saudiyya ba tare da izini ba.

Dr Ibrahim Kana ya ce mahajjatan, wadanda 'yan jihar Ogun ne, na yawon bude ido ne a garin Makkah amma sai suka hau hanyar da za ta kai su kasar Yemen inda a nan ne askarawa Saudiyyar suka kama su.

Sai dai ya ce daga bisani hukumomin Saudiyyar sun saki mahajjatan.

Saudiyya dai ta tsaurara matakan tsaro a kan iyakarta da Yemen saboda rikicin da ake fuskanta a kasar.