Nigeria: Wa'adin asusun bai-daya ya cika

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun bayan hawansa mulki shugaba Buhari ya fara kokarin bullo da matakai don yakar rashawa

A ranar Talata ne wa'adin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta debawa ma'aikatun gwamnatin kasar na fara amfani da asusu na bai-daya yake cika.

Gwamnati ta bayar da umarni ga dukkan ma'aikatunta da su sanya kudaden da ke shigo musu a asusun da ke babban bankin kasar a kokarin da take yi na magance cin hanci da rashawa da suk addabi kasar.

Rahotanni dai na nuna cewar da alama wasu ma'aikatun gwamnatin ba za su iya cimma wa'adin ba.

Sai dai gwamnatin ta ce za ta hukunta duk ma'aikatar da ta kasa cimma wannan wa'adi.

Masana tattalin arziki dai na ganin cewa wannan tsari na asusun bai-daya yana da matukar amfani kuma zai bai wa gwamnati dama ta san ainihin yawan kudaden da suke shiga aljihunta.