'Yan gudun hijira: Hungary za ta gina shinge

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan gudun hijirar Syria na ci gaba da kwarara Turai

Hungary ta ce tana shirin gina wani shingen waya a kan iyakarta da kasar Romaniya.

Ministan harkokin wajen Hungary Peter Szijjarto, ya ce za a kara nisan katangar da kasar ta gina a kan iyakarta da Serbia a baya-bayan nan, saboda a hana kwararar da da 'yan gudun hijira ke yi ba kakkautawa.

Tun da farko dai Hungary ta ayyana dokar ta baci a gundumomin kudancin kasar da ke iyaka da Serbia inda wani gungun 'yan gudun hijira fiye da 250 suka yi dafifi suka kuma ki ci ko sha da zummar sai an bar su sun shiga kasar.

A bangare daya kuma shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta nemi a yi wani taron gaggawa na Shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai a cikin mako mai zuwa don tattauna matsalar 'yan gudun hijira.

Ta ce sai kungiyar ta EU ta yi aiki tare ne kawai za a iya warware matsalar.