Hatsarin Makkah: Saudiyya ta fara daukar mataki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Injin din ya fado ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sharara.

Hukumomin Saudiyya sun dauki mataki a kan kamfanin gine-gine na Bin Laden, bayan da wani babban injin yin gini ya fado a masallacin Harami da ke Makkah.

Kafofin yada labarai na kasar Saudiyya sun ruwaito cewar gwamnatin kasar ta ce daga yanzu ta dakatar da bai wa kamfanin Bin Laden, wanda yana daya daga cikin manyan kamfanonin gine-gine na kasar kwangilar gini, har sai an kammala bincike.

A ranar Juma'a ne hatsarin ya faru wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 100.

Injin din ya fado ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sharara.

Lamarin ya faru 'yan makonni kafin gudanar da Arafa a yayin da maniyyata daga kasashe daban-daban na duniya suka hallara a kasar domin sauke farali.