Sojin Kamaru da Boko Haram sun yi barna — Amnesty

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Amnesty International ta ce Boko Haram ta kashe fararen hula a kalla 400 a Kamaru a wannan shekarar.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta zargi sojin Kamaru da kungiyar Boko Haram da tafka barna a kasar ta Kamaru.

Amnesty ta ce Boko Haram ta kashe fararen hula akalla 400 da kuma sojoji da dama a wannan shekarar.

Ta kara da cewa jami'an tsaron kasar sun yi wa fiye da mutane dubu daya kawanya, sannan suka kashe wasu daga cikin su a matsayin ramuwa a kan hare-haren 'yan Boko Haram.

Boko Haram dai ta fi kai hare-hare a Najeriya -- wacce ita ma ake zargin jami'an tsaronta da cin zarafin jama'a -- amma kungiyar tana kai hare-hare a kasashen Kamaru da Jamhuriyar Nijar da Chadi.