Na daina harkokin siyasa — Bamanga Tukur

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bamanga Tukur ya ce ya bai wa sabbin-jin damar ba da gudunmawarsu a siyasa.

Tsohon shugaban jam'iyyar PDP a Najeriya, Alhaji Bamanga Tukur, ya ce ya daina harkokin siyasa.

Bamanga ya bayyana haka ne a wani taron lacca da aka gudanar a kan cikar sa shekaru 80 a duniya.

A cewar sa, yanzu lokaci ne da ya kamata ya huta domin bai wa sabbin-jini damar taka tasu rawar a harkokin siyasar kasar.

Bamanga Tukur ya rike mukamai da dama a shekarun da ya kwashe yana yin siyasa, ciki har da gwamnan tsohuwar jihar Gongola da kuma yin takarar shugabancin kasar.

A shekarar 2014 ne ya sauka daga shugabancin jam'iyyar PDP bayan ya sha matsin-lamba daga wajen gwamnoni da ma wasu manyan jam'iyyar.