Facebook zai bullo da madannin "Dislike"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Madannar 'dislike' da za a bullo da ita a Facebook

Mutumin da ya kirkiro shafin sada zumunta na Facebook, Mark Zuckerberg, ya ce shafin zai bullo da alamar da mutane za su rika latsawa domin nuna rashin "so" ko gamsuwa da abubuwan da wasu za su rika yadawa a shafin.

A wajen wani taron tambayoyi-da-amsa a shedkwatar shafin Facebook a California, Mista Zuckerberg ya ce matsalar alamar wata hanya ce da mutane za su rika bayyana yadda suke ji.

Ya ce shafin na Facebook yana gab da ya fara gwajin sabuwar alamar.

Wasu masu amfani da shafin Facebook sun jima suna nuna bukatar a bullo da alamar tun bayan da aka bullo da alamar nuna "so" ko gamsuwa da abubuwan da sauran mutane ke yadawa a shafin a shekarar 2009.

"Mutane sun dade suna tambaya game da bullo da malatsar alamar nuna rashin so ko gamsuwa a shafin", in ji Mista Zuckerberg.

Zuckerberg ya kara da cewa, "Daruruwan mutane sun nuna bukatar a bullo da alamar, kuma yau rana ce mai muhimmanci tun da a yau ne nake sanar da cewa muna aiki domin tabbatar da hakan".

Sai dai Mista Zuckerberg ya ce ba ya son madannin 'dislike' ya zamo hanyar da mutane za su rika kaskantar da rubuce-rubucen da wasu za su rika yi a shafin na Facebook.