Ghana: Ana zanga-zanga a kan rijistar zabe

Image caption Masu goyon bayan jam'iyyar adawa sun bukaci a yi sabuwar rajistar zaben kasar Ghana.

Magoya bayan jami'yyar adawa masu matsin lamba sun yi jerin gwano a Accra, babban birnin Ghana inda suka bukaci a yi sabuwar rijistar zabe kafin zaben kasar da za a yi badi.

Jami'yyar adawa mafi girma ta New Patriotic, tana zargin 'yan kasashen Togo da Burkina Faso mazauna Ghana da kuma yara wadanda shekarunsu bai kai yin zabe ba sune a kan rijistar zaben.

Sai dai Jamiyya mai mulki ta National Democratic Congress, ta yi watsi da bukatar a yi sabuwar rijistar masu kada kuri'a.

Rahotannin sun ce akwai 'yan sanda da dama a wajen zanga-zangar.

A ranar Talata ne wata kotu a Ghana ta bai wa 'yan sanda damar hana 'yan zanga-zangar yin jerin gwano a gaban ofishin hukumar zaben bisa dalilan tsaro.