Hungary ta fara tantance 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An fara tantance 'yan hijrar bayan sun kwana a bakin iyakar kasar

Kasar Hungary ta fara shiri na gaggauta duba takardun neman mafaka da masu kaura zasu gabatar a hanyoyin shiga kasar ta kudanci.

Hukumomin Hungarin sun ki amincewa da rukunin farko na masu neman mafaka wadanda suka fito daga Bangladesh, saboda sai da mutanen suka wuce ta Serbia, wadda Hungarin take gani nan ma mafaka ce ga masu kaurar.

Masu kaura da yawa ne suka shafe daren ranar Talata a bakin iyakar kasar Serbia da Hungary, bayan hukumomi a Hungarin sun rufe hanyoyin shiga kasar.

'Yan sandan kasar sun ce 'yan gudun hijira fiye da 400 ne suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba ranar Talata.