Darajar Naira ba za ta sake faduwa ba — Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Buhari ya ce ba ya tunanin darajar naira zata sake yin kasa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba ya tunanin darajar naira za ta sake yin kasa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar da ya yi da gidan talbijin na France 24 ranar Laraba a birnin Paris.

Shugaba Buhari ya ce, "Ina ganin darajar naira ba za ta sake faduwa ba; hakan ba zai haifarwa Najriya da mai ido ba. Shi ya sa muke so babban bankin kasa CBN ya yi sauye-sauye a hanyoyin samar da kudaden kasashen waje domin gudanar da muhimman ayyuka.

Babban bankin kasar yana kara tsuke damar samun kudin kasashen waje, a wani kokari na farfado da darajar naira.

A watan Yuni ne CBN ya toshe duk wata hanyar samun kudaden kasashen waje, inda ya hana shigo da abubuwan amfani 41 cikin kasar daga wasu kasashe.