Ana cin zarafin yara sosai a Nigeria

Image caption Cin zarafin yara na yawaita a Najeriya

Wani rahoto da hukumar kidaya ta Najeriya ta fitar ya nuna cewa kashi 60 cikin 100 na yara a kasar suna fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata da su.

Bincike, mai taken "Violence Against Children," wato cin zarafin yara, wanda aka gudanar da shi da taimakon Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya da kuma cibiyar kare yaduwar cututtuka ta Amurka, shi ne irinsa na farko a Najeriya da ma Afrika ta Yamma.

Binciken ya kuma gano cewa iyaye ko dangi na kusa su suka fi cin zarafin yara ta hanyar dukansu ko kona su da gangan ko kuma cin zalinsu ta hanyoyi daban-daban.

Su kuwa yara mata suna fuskantar cin zarafi ne ta hanyar lalata da su da ake yi tun a shekarun kuruciyarsu. Daya daga cikin ko wadanne yara maza 10 kuwa na fuskantar cin zarafi inda su ma ake samun makwabta ko abokan karatunsu na lalata da su.

Rahoton ya bayar da shawara cewa ya kamata gwamnati ta yi kokarin sauya tunanin mutane dangane da cin zarafin yara.

Ya kuma bukaci a karfafawa yara gwiwa su dinga fadar irin cin zarafin da ake musu da kuma masu aikata musu hakan.