Matsin lamba ba zai sa na bar mulki ba - Assad

Hakkin mallakar hoto SANA
Image caption Shugaba Assad na kasar Syria ya ce ba zai sauka daga mulki ba tamkar 'yan kasar basu bukace shi da yin haka ba.

Shugaban Syria Bashar al-Assad, ya ce ba zai sauka daga kan mulki ba saboda matsain lambar kasashen yamma, sai dai idan 'yan kasar ne suka ce ba su yarda ya ci gaba da mulkin ba.

A lokacin da shugaba Assad ya ke yiwa manema labarai na Rasha jawabi ya ce tururuwar da 'yan Syria suke yi zuwa kasashen Turai na faruwa ne saboda 'yan gudun hijirar suna gudun ta'addanci ba gwamnatinsa ba.

Shugaba Assad ya yi wannan jawabin ne kwana daya bayan shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bukaci sauran kasashe su bi sawun kasarsa wajen goyon bayan gwamantin shugaba Assad.

Sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry, ya ce idan Rasha ta ci gaba da marawa Mista Assad baya, akwai hadarin rikicin kasar zai kara daukar tsawon lokaci kafin a shawo kansa.