Yaron da aka zarga da haɗa bam ya ɗaukaka

Hakkin mallakar hoto ANIL DASH

A Amurka 'yan sanda a Texas sun yi watsi da tuhumar da suke yi wa wani yaro ɗan shekaru 14 a game da wani agogo da ya ƙirƙiro wanda suka ce ya yi kama da bam.

Ahmed Muhammed ya na da sha'awar kirkiro abubuwa, dan haka ne ya hada agogo da kansa a gida kuma ya kai agogon makaranta domin ya burge malamansa da 'yan ajinsu.

Maimakon ya burge su sai aka kira 'yan sanda domin su bincike shi domin abinda suke zaton ƙoƙari ne na haɗa bam.

Yanzu babban jami'in 'yan sanda ya ce, babu wata shaidar cewa, Ahmed yana kokari ne ya aikata ba daidai ba. Dan haka aka kashe maganar.

Amma wannan al'amari ya janyo cece kuce sosai.

Wasu musulmi sun ce, anyi Ahmed wannan zato ne saboda shi musulmi ne, amma 'yan sanda sun musanta wannan zargi.

Amma yanzu haka Ahmed dan shekaru goma sha hudu yana cigaba da samu goyon baya a kafofin sada zumunta na Internet inda Hillary Clinton ta rubuta a shafinta na Twitter cewa, 'Ahmed ka ci gaba da hazakar kirkiro abubuwa.'

Mahaifin Ahmed wanda asalinsa dan Sudan ne ya ce, an yiwa dansa zaton hada bam ne saboda shi musulmi ne.