Croatia ta taka wa 'yan gudun hijira birki

'Yan gudun hijira a kasar Croatia Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan gudun hijira a kasar Croatia

Kasar Croatia ta ce baza ta iya daukar karin wasu 'yan gudun hijira ba, inda ta nemi sojojinta da su zama a cikin shirin ko ta kwana.

An samu hatsaniya a garin Tovarnik dake kan iyaka, inda 'yan sanda ke ta fama da dubban mutane dake san nausawa Turai bayan da suka zo daga Serbia.

A cikin tsananin rana mutanan ke ta ihun " muna san mu tafi, muna san mu tafi" kuma wasu jerin matasa su ka yi kokarin balla layin da 'yan sanda suka ja.

Ministan cikin gidan kasar ya ce tilas ne 'yan gudun hijirar da ke cikin Croatia su nemi mafaka ko kuma a dauke su a matsayin bakin haure.