Kuroshiya ta koka da yawan 'yan gudun hijira

'yan gudun hijirar a Hangare Hakkin mallakar hoto AP

Kasar Kuroshiya ta ce ba za ta iya daukar karin wasu 'yan gudun hijira ba, kuma ta nemi sojojinta da su zama a cikin shirin ko-ta-kwana, ko da za a bukace su su tsare kan iayakar kasar.

An samu hatsaniya a garin Tovarnik da ke kan iyaka inda 'yan sanda ke ta fama da dubban mutane dake son nausawa Turai bayan da suka isa kan iyakar kasar da Sabiya.

A cikin tsananin rana mutanen ke ta ihun "Muna son mu tafi, muna son mu tafi" kuma wasu jerin matasa su kai kokarin balla layin da 'yan sandan suka yi.

Ministan cikin gidan kasar ya ce tilas ne 'yan gudun hijirar da ke cikin Kuroshiya su nemi mafaka ko kuma a dauke su a matsayin bakin haure.