'Yan ci-rani 8,000 sun isa Jamus

Hakkin mallakar hoto AFP getty
Image caption 'Yan ci rani

Rahotanni daga Jamus na cewa kusan 'yan ci-rani 8,000 ne suka isa jihar Bavaria da ke kudu maso gabashin kasar a ranar Laraba.

Hukumomi a Jamus sun kara dawo da bincike a kan iyakar kasar a karshen makon jiya domin su takaita adadin 'yan ci-ranin da ke shiga kasar.

A ranar Alhamis da safe 'yan sanda sun tsare daruruwan mutane a kan iyakar kasar da Austria.

A halin da ake ciki, shugaban hukumar kula da shige da fice na kasar Jamus ya yi murabus.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ce Manfred Schmidt ya yi murabus ne saboda wasu dalilai na kashin kansa.

Ofishinsa, wanda ke kula da kaurar baki da 'yan gudun hijira, ya fuskanci suka saboda jinkiri wajen samar da mafaka ga 'yan-cirani.