ISIS na jawo hankulan 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan gudun hijirar Syria na tururuwar shiga Turai

Mayakan kungiyar IS sun yi ta saka bidiyo a shafukan intanet inda suke rokon musulman da ke gudun hijira da su shiga cikin kungiyar, maimakon abin da suka kira "yin kaura zuwa kasashen Turawa kafirai".

Sun tura bidiyon ne da zummar lallashin 'yan gudun hijirar da cewa za su fuskanci tsangwama da wariyar launin fata a Turai.

Tun lokacin da aka kafa kungiyar IS a Syria, mutane da dama sun yi ta kokarin tserewa daga kasar inda da yawan mutane ke tsoron fadawa karkashin ikon mayakan.

Amma a bidiyon kungiyar IS ta ce zai fi wa 'yan gudun hijirar rufin asiri su tafi yankunan da ke karkashin ikonta inda nan ne ake yin musulunci kan hanya ta daidai.