Sojoji sun rushe gwamnati a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin sun yi garkuwa da Mr Kafando.

Sojoji a kasar Burkina Faso sun rushe gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin shugaba Michel Kafando a wani abu da ake gani tamkar juyin mulki ne.

A jawabin da wani jami'in soja ya yi ta kafar watsa labaran gwamnati ya ce, "Mun kafa wata majalisar tabbatar da dimokradiyar wacce ke da alhakin shirya zabe babu nuna bambamci."

A ranar Laraba ne wasu sojoji suka katse zaman majalisar ministocin Burkina Faso, suka kuma tsare wasu mistoci biyu tare da shugaban gwammnatin rikon-kwarya Michel Kafando da kuma Firai minista Isaac Zida.

Wannan abin da suka aikata ya zo ne kwanaki biyu bayan wani kwamiti na hukumar sauye-sauye na majalisar rikon kwaryar ya fitar da rahotonsa a inda ya ce dakarun fadar shugaban kasar sun zama tamkar wata rundunar sojoji a cikin sojojin kasar da ya kamata a wargaza su.

Tuni dai Amurka da kungiyar Tarayyar Turai suka bukaci sojojin su saki wadannan shugabannin biyu.

Sa toka sa katsi na baya-bayanan dai, ya zo ne kasa da wata guda kafin zaben shugaban kasar da na 'yan majalisu wanda zai kawo karshen mulkin rikon kwarya a kasar wanda aka kafa a sakamakon tarzomar da ta yi waje da Blaise Compaore wanda ya yi mulki na tsawon shekara 27.

An dai shirya gudanar da zabukan ne a ranar 11ga watan Oktoba.