NDLEA ta kama masu fasa kwaurin dala

Hakkin mallakar hoto NDLEA
Image caption Hukumar NDLEA ita ce mai yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta kama wadansu mutane shida da suka kware wajen hadiyar dalar Amurka, a kokarinsu na fita da ita kasashen waje.

Wannan dai shi ne karon farko da jami'an hukumar suka kama mutane da wannan sabon salon fataucin haramtattun kudade da suka bullo da shi.

Mai Magana da yawun hukumar, Michael Ofeyoju, ya ce an samu dala 156,000 a hannun mutanen bayan da jami'an NDLEA suka dirar musu a wani otel inda aka yi musu kofar-rago.

Mista Ofeyoju ya kara da cewa kafin zuwan jami'an tuni mutanen sun riga sun hadiye dala 111,000.

Hukumar ta NDLEA ta ce wannan salo ya zo musu da ba-zata, bisa la'akari da cewa an fi sanin masu fataucin miyagun kwayoyi da mulmula hodar Ibilis su hadiye.