Wani mutum ya tafi Hajji a kafa

Image caption Wannan ne karo na uku da Al-Qahtani ya je aikin hajji a kafa

Wani dan kasar Saudiyya da ya taba zuwa aikin Hajji a kafa a shekaru biyu a jere a madadin mahaifiyarsa, Yarima Naif, a bana ma ya dauki haramar yin hakan, amma wannan karon zai yi hajjin ne a madadin tsohon Sarkin kasar Abdul Aziz.

Kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito cewa Nasser Jarallah Al-Qahtani, ya taho daga garinsa Khamis Mushayet zuwa Riyadh a mota, daga nan kuma sai ya fara tafiyar kafa daga makabartar Al-Oud ranar 24 ga Agusta.

Ana sa ran zai isa Makkah ranar Talata.

An yi ta sa bidiyo da hotunan mutumin a shafukan intanet yayin da yake tafiyar dauke da tutar Saudiyya a bayansa.

Matakin da Al-Qahtani ya dauka na yin aikin hajji a kafa da kuma yadda ya ki yarda da kowanne taimako ya bai wa 'yan kasar Saudiyya da dama mamaki.