Gobara ta kashe mutane 170 a Sudan ta Kudu

Image caption Mutanen sun je ne domin diban mai daga cikin motar.

Jami'ai a kasar Sudan ta kudu sun ce gobarar da wata motar dakon man fetur ta haddasa ta kashe mutane sama da 170.

Jami'an sun kara da cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon hatsarin.

A cewar su, mutanen sun ruga aguje wajen da motar da fadi domin su dibi man da ke kwarara a garin Maridi da ke jihar Western Equatoria, sai kawai ta kama da wuta.

Gwamnan jihar ya yi kira ga kungiyar bayar da agaji ta Red Cross da kuma Majalisar Dinkin Duniya su taimaka musu, yana mai cewa lamarin ya yi kamari.