Nigeria ta hadu da Niger a Warisha

Image caption Wasu manyan jami'an gwamnatin Jamhuriyar Nijar da kuma Mai shirya fim din Warisha a bikin kaddamar da daukar fim din a Yamai Jamhuriyar Nijar

Wani kamfanin shirya fina-finai a Nigeria ya tare a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar domin daukar wani fim mai suna Warisha a karo na farko a tarihin kasashen biyu.

A hirar da ya yi da BBC wanda ya shirya fim din Mika'ilu Isah, wanda aka fi sani da Gidigo, ya ce sun shirya fim din ne a Nijar domin kara dankon zumunta tsakanin kasashen biyu.

An dauki kimanin wata 10 ana tsara fim din a Najeriya kafin a je Yamai daukarsa a faifan bidiyo.

Ana sa ran daukar kimanin watannin 2 wajen hada hoto da kuma tace fim a Najeriya.

A cewar sa, za a fassara fim din a cikin harshen Faransanci da Ingilishi da kuma harshen Swahili domin yada shi a tashoshin wasu gidajen talbijin na Afrika.

Aminu Dagash, daya daga cikin jaruman fim din, ya shaida wa BBC cewa labarin Warisha mai bangare-bangare ne, watau Series.

Ya ce fim din ya hada fittatun 'yan wasan kwaikwayo na Jamhuriyar Nijar da na Najeriya wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen isar da sakon sa.

An kuma yi amfani da kayan aiki na zamani wajen daukar shirin gami da kwararrun ma'aikata domin fim din ya yi gogayya da kowanne irin fim a duniya, a cewarsa.