Kuroshiya za ta kori 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan gudun hijira na neman shigowa Croatia a hanyar su ta zuwa Turai.

Firayi Ministan Kuroshiya Zoran Milanovic ya gargadi 'yan gudun hijira da ke tururuwa zuwa kasar da cewa zai kora su, domin a cewar sa, kasar ba za ta zama "matattarar su ba".

Shugaban ya ce kasar sa ba za ta rufe kan iyakar ta gaba daya ba, amma ta daina karbar karin 'yan gudun hijira.

Jawabin Milanovic na zuwa ne a lokacin da Kuroshiya ta rufe bakwai daga cikin hanyoyi takwas da 'yan gudun hijira ke bi wurin shiga kasar a kan hanyar su ta shiga Turai.

Sama da mutane 14,000 ne suka shiga Kuroshiya a galabaice kuma cikin matsanancin hali.

'Yan gudun hijira da yawa da suka doshi arewacin yankin Balkans sun janyo cece-ku-ce a tsakanin kungiyar Tarayyar Turai.