Kenya: Yajin aiki zai shafi dalibai miliyan 12

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Uhuru Kenyatta, Shugaban kasar Kenya

Kusan dalibai miliyan 12 ne za a tirsasawa zaman gida bayan da gwamnatin Kenya ta bayar da umarnin a rufe makaratun kasar daga ranar Litinin a mako mai zuwa, sakamakon yajin aiki da Malamai suka shafe makonni uku suna yi.

Daliban da suke rubuta jarabawar gama makaranta ne kawai za a barsu su je makaranta.

A watan da ya gabata ne kotun koli ta Kenya ta yanke hukunci cewa gwamnatin kasar ta karawa Malamai albashi da a kalla kaso 50 cikin 100.

Sai dai gwamnatin Kenyar ta yi watsi da hukuncin inda ta ce bata da kudin yin hakan.