An kashe mutane 8 a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hari a Pakistan

Rundunar Sojin Pakistan ta ce ta dakile wani kokarin hari da wasu 'yan bindiga suka kai a sansanin sojojin sama dake wajen birnin Peshawar a arewa maso yammacin kasar.

Rundunar ta ce sama da 'yan bindiga 10 ne suka yi yunkurin shiga sansanin in da suka kai hari dakin tsare mutane .

Majiyar rundunar sojin ta ce akalla mutane 8 sun mutu a yayin musayar wutar, yayin a loakci guda kuma wasu 20 sun jikkata daga cikin su akwai sojoji 10.

Kungiyar Taliban dai ta dauki alhakin kai harin.

Peshawar dai ta kasance daya daga cikin wuraren da 'yan bindiga ke kai wa hari.

Ko a watan Disambar 2014 sama da 'yan makaranta da malamai 150 kungiyar Taliban din ta kashe a wani hari da 'ya 'yanta suka kai a wata makaranta.