Paparoma ya bai wa 'yan gudun hijira masauki

Image caption Paparoma Francis

Wadansu na hannun daman Paparoma Francis sun ce ya bai wa iyalan 'yan gudun hijira na Syria masauki a fadar Vatican.

Iyalan, wadanda suka hada da mahaifi da mahaifiya da kuma yaransu biyu sun zo ne daga Damascus kuma su mabiya darikar Katolika ta kasar Girka ne wadanda suke da kusanci da mabiya Cocin Roman Katolika.

Su ne iyalai na biyu da Paparoma Francis ya yi wa alkawarin muhalli a kokarin sa na taimakawa kasashen Turai wajen bayar da agaji don kawar da matsalar 'yan gudun hijira da su ke fuskanta.