Shekau ya yi wa sojin Nigeriya raddi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau ya musanta nasarorin sojin Nigeria akan kungiyarsa.

Jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya fitar da wani faifan muryarsa ta hanyar intanet yana musanta ikirarin rundunar sojojin Nigeria cewar tana samun galaba akan 'yan kungiyar.

Abubakar Shekau ya musanta cewa akwai wasu 'yan kungiyar da ke gidan yari da suka dawo daga rakiyarta.

Ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da sojin najeriyar su ke cewa suna dab da kawar da kungiyar ta Boko Haram.

A sanarwar da kakakin rundunar sojan kasa, Kanar Sani Kuka Sheka Usman ya fitar ya ce dakarunsu sun kame kauyukan Jerre da Dipchari, kana su ka lalata sansanonin 'yan Boko Haram da ke yanki.

A cewarsa, dakarun da ke yankin Bama sun ceto karin mutane 62. Ya kara da cewa dakarun nasu suna ci gaba da tsefe yakunan Bama da Banki da Pulka domin yiyuwar kawar da gyauron 'yan Boko Haram da suka rage a yankin.