Boko Haram ta raba yara 1.4 m daga gidajensu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption UNICEF ta ce yara miliyan daya da dubu dari biyu Boko Haram ta kora daga gidajensu a Najeriya.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta ce Boko Haram ta raba yara 1.4 m daga gidajensu a Najeriya da makwabtanta.

A wani sabon rahoto da ta fitar, hukumar ta ce hare-haren kungiyar sun tilasta wa kananan yara 500,000 barin gidajensu a cikin watanni biyar da suka wuce.

A cewar ta, hakan ya zo daidai da lokacin da kungiyar ke ci gaba da kai hare-hare a Najeriya da makwabtanta -- Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi.

UNICEF ta ce a arewacin Najeriya kadai, yara miliyan daya da dubu dari biyu, wadanda rabinsu ba su wuce shekaru biyar ba, Boko Haram ta raba da gidajensu.

Ta kara da cewa yaran suna fama da wahala wajen samun taimako.

UNICEF ta ce tana kula da lafiyar yaran da ke fama da matsananciyar yunwa, sannan tana ba su tsaftataccen ruwan sha.

Hukumar ta kara da cewa tana taimakawa domin ganin dubban yaran sun ci gaba da zuwa makaranta.

Sai dai hukumar ta ce ba ta samun isasshen kudin da take gudanar da ayyukanta.