'An warware juyin mulkin Burkina Faso'

Hakkin mallakar hoto
Image caption An mayar da Michel Kafando Shugaban rikon kwarya a Burkina Faso kan kujerar shugabancin kasar bayan da masu shiga tsakani sun sa baki a juyin mulkin da aka yi a kasar

A ranar Asabar ne mai shiga tsakani na kungiyar ECOWAS Boni Yayi kuma shugaban Benin ya sanar da cewa sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Fason sun amince da kasar ta koma mulkin farar hula.

A cewar wani babban jami'in majalisar gwamnatin rikon kwaryar kasar, yarjejeniyar da aka cimma ta shardanta cewa shugaban kasar na rikon kwarya ya koma kan karagar mulki kuma a gudanar da zabe a cikin makonni masu zuwa.

Ana dai cigaba da tattaunawa a babban birnin kasar, Wagadugu, kuma masu shiga tsakanin suna tattaunawar da bangaren adawa.

Wakiliyar BBC ta ce ba kasafai ba dai ake warware juyin mulki a Afirka, amma wannan karon shugaban Senegal da takwaransa na Benin suna shiga tsakani ne da goyon bayan kasashen duniya.

Ana dai ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da tumbuke gwamnatin rikon kwarya da Michel Kafando ke jagoranta.

Ma'aikatan asibiti sun ce an kashe mutanen da suka kai goma.

Wani mazaunin birnin Wagadugu ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa harkoki sun tsaya a birnin saboda zanga-zangar da ake yi.

Karin bayani