Paparoma ya soma ziyara a Cuba

Hakkin mallakar hoto REUTERS

Mabiya cocin Roman Katolika a Cuba sun hallara a Havana babban birnin kasar, inda suka tarbi Paparoma Francis wanda ya kai ziyararsa ta farko a ƙasar.

Wannan dai shi ne masomin ziyarar kwanaki goma da Paparoman zai yi a Cuban da kuma Amurka.

Paparoman wanda yake da ra'ayin kare masu ƙaramin ƙarfi da sukan tsarin jari-hujja ya samu karbuwa a wajen shugaban Cuba Raul Castro wanda zai tarbi Paparomin a filin jiragen sama na Havana.

Sai dai kuma irin ra'ayoyin Paparoma Francis basu samu karbuwa ba a Amurka, amma duk da haka yana da farin jini musamman tsakanin wadanda suke da alaka ta asali da Spaniya.