Sojin Nigeria sun ceto mutane 90

Hakkin mallakar hoto nigeria defence forces
Image caption Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto mutane 90 bayan da ta tarwatsa 'yan Boko Haram daga kauyuka biyu a arewa masogabashin kasar.

Kakain rundunar sojan kasa ta Najeriya, Kanar Sani Usman Kukah Sheka ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya aikewa manaema labarai.

A cewar sa, rundunar ta ceto maza 23 da mata 33 da kuma yara 34 daga hannun 'yan Boko Haram a ranar Alhamis a kauyukan Dissa da Balaza garin Gwoza a jihar Borno.

Kanar Kuka Sheka ya kara da cewa Rundunar ta sake bude wata makaranta a Goza wacce a da aka rufe ta hare-haren 'yan Boko Haram.