Jirgin sojin Venezuela ya fado

Hakkin mallakar hoto AirTeamImages.com
Image caption Jirgin sama

Gwamnatin Venezuela ta ce wani jirgin saman yakin soja ya yi hadari a kan iyakar kasar da Columbia a lokacin da yake kora wani jirgin da ba a gane daga ina yake ba.

Dukkanin matuka jiragen sun mutu.

Ministan tsaron kasar Vladimir Padrino Lopez ya ce jirgin sojan kasar ta su ya tisa keyar dayan jirgin ne bayan da ya shiga sararin samaniyar kasar su inda ya nufi kudancin kasar.

Mr Padrino ya kara da cewa wajen da jirgin ya nufa ya yi kaurin suna wajen masu safarar miyagun kwayoyi.