Banki ya ware 2bn don masu shirin fim

fim
Image caption Wasu masu shirin fim a bakin aiki

Bankin masana antu na Nigeria BOI ya ware Naira biliyan 2 a matsayin bashi ga masu sana ar shirya fina-finai a Nigeria.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban bankin Rasheed Olaoluwa yayin da ya kai ziyara inda ake daukar wani fim a Legas.

Shugaban bankin ya ce 'masu shiryawa fina-finan na kasar za samu rancen kudin ne domin su samu damar shirya fina-finan da suka amsa sunansu, wadanda kuma za a iya nuna su a ko ina a duniya.

Sannan ya kara da cewa bankin ya inganta ayyukansa domin saukakawa masu shirin fim din cin gajiyar bashin ta hanyar la akari da yadda yanayin sana ar shirin fim ya ke.

Bankin in ji shi, ya yi sassauci ga wasu sharuddan bayar da bashin saboda masu sana ar su samu damar karbar bashin, haka kuma bankin na duba wasu hanyoyin biyan bashin da suka sha ban ban da na sauran masana antu.

Fina-finan Najeriya dai musamman na arewacin kasar na shan suka kan yadda ake yin su, lamarin da masu sana'ar ke cewa rashin isasshen kudi ne.