Al'ummar Girka za su kada kuri'a a yau

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Zabe a kasar Girka

Al'ummar kasar Girka na tafiya zuwa rumfunan zabe domin kada kuri'un su a babban zaben kasar karo na 5 a cikin shekaru 6.

Shugaban jam'iyyar Syriza mai ra'ayin rikau wato tsohon firaministan kasar Alexis Tsipras ya yi kiran da a gudanar da zaben gaggawa bayan jam'iyyar sa ta rasa kujerun 'yan majalisar dokokinta da dama.

Masu jin ra'ayin jama'a akan zaben sun ce za a iya yin kankankan a tsakanin manyan jam'iyyun kasar biyu wato Syriza da kuma jam'iyyar New Democracy.

Zaben dai na zuwa ne a cikin wani mawuyacin yanayi kasancewar kasar na dab da cika wa'adin da aka dibar mata na aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu kamar yadda aka cimma yarjejeniya akarkashin batun ceto kasar daga kangin bashin da ya yi mata katutu tare da kungiyar tarayyar turai